Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin KTT Ta Ce Tilas A Yi Da Yasser Arafat - 2002-02-07


Majalisar dokokin Tarayyar turai tana kara matsin lamba kan Isra’ila da ta ci gaba da yin aiki tare da Majalisar Mulkin kai ta Falasdinawa a zaman abokiyar shawarar neman zaman lafiya. Wani kudurin da aka zartas yau alhamis a zauren majalisar a birnin Strasbourg, ya ce Isra’ila tana bukatar Majalisar Falasdinawan da kuma shugabanta Yasser Arafat a zaman abokan neman zaman lafiya.

Firayim ministan Isra’ila, Ariel Sharon, yana dorawa Malam Arafat laifin hare-haren kunar bakin waken da ake kaiwa Isra’ila, yana kuma kokarin ya maida shi saniyar ware.

Majalisar dokokin KTT tayi kira ga dukkan sassan da su dauki matakan kawo karshen zub da jini tsakanin Isra’ila da Falasdinawa nan take. Musamman majalisar ta ambaci hare-haren ta’addanci kan fararen hula ’yan Isra’ila, da kashe-kashen gillar da sojojin Isra’ila keyi da kuma lalata kayayyakin bukatu na Falasdinawa.

Ana sa ran batun mai sarkakiya na kokarin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya zai sha gaban sauran batutuwa idan ministocin harkokin kasashen wajen KTT sun gana a ranakun Jumma’a da asabar a Spain. Rahotanni sun ce KTT tana shirya wani yunkuri na farfado da shirin samar da zaman lafiyar.

XS
SM
MD
LG