Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun kai Farmaki Cikin Yankunan Falasdinawa - 2002-02-08


Rundunar sojojin Isra’ila ta ce dakarunta dake samun kariyar tankoki, sun kai farmaki cikin sassan da Falasdinawa ke mulkinsu a Yankin yammacin Kogin Jordan, inda suka kama ’yan kishin Falasdinu uku.

Wannan farmaki da aka kai cikin dare da kuma asubahin yau, martani ne a bayan harin da wani Bafalasdine dan bindiga ya kai ranar laraba, inda ya kashe ’yan Isra’ila uku a wata unguwar share-ka-zauna ta Yahudawa kusa da Nablus.

A wani labarin dabam na tashin hankali, an kashe wani Bafalasdine cikin dare kusa da wani wurin binciken ababen hawa da sojojin Isra’ila suka kafa a kan hanya a wajen birnin Bethlehem.

Jiya alhamis a fadar White House, shugaba Bush ya shaidawa firayim minista Ariel Sharon na Isra’ila cewar Amurka zata ci gaba da matsawa shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, kan ya dauki matakan murkushe masu tsattsauran ra’ayi.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida, Mr. Bush ya ce zai ci gaba da kokarin shawo kan Malam Arafat ya san cewa tilas ne ya dauki kwararan matakai na zahiri domin rage ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya. A daidai wannan lokacin kuma, shugaba Bush ya ce dole ne a taimakawa Falasdinawan da babu hannunsu a ayyukan ta'addanci da kudi ta yadda azasu kyautata rayuwarsu.

XS
SM
MD
LG