Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Suna Ganawa da Shugaba Chirac a Paris - 2002-02-08


Shugaban Faransa, Jacques Chirac, ya kaddamar da zaman tattaunawa da shugabannin wasu kasashen Afrika 13, a gameda sabuwar hobbasar diflomasiyya ta habaka tattalin arzikin nahiyar Afrika.

Mr. Chirac ya shaidawa taron da ake yi yau a birnin Paris, cewa, agajin da kasashen ketare suke baiwa Afrika yana ja baya, a wani mizani da bai dace ba. Ya ce, shugabannin kasashen nan takwas masu cigaban masana’antu, da Rasha, sun yi alkawarin bullo da wani sabon shirin kawance da Afrika, kuma za su tattauna batun, a taron kolinsu na gaba da za su gudanar a kasar Canada, cikin watan yunin bana.

Tattaunawar da ake yi a Faransa kuwa, tana mayar da hankali ne gameda wani shiri mai suna "sabon shirin kawancen habaka nahiyar Afrika." Shirin, wanda shugabannin kasashen Nijeriya, Masar, Afrika ta Kudu, Senegal, da kuma Aljeriya suka tsara, yana kokarin ganin kasashen yamma sun zuba wani jari na dala milyan dubu 64 a Afrika, domin farfado da tattalin arzikin nahiyar da yake cikin kunci.

Kungiyar wadannan kasashe na Afrika, ta ce, ana bukatar mizanin habakar tattalin arzikin Afrika ya rika kai kashi bakwai cikin dari kowace shekara, domin raya tattalin arzikin nahiyar, inda kowane mutum daya, a mutane milyan 800 yake dogara kan kudi kasa da dalar Amurika guda domin gudanar da harkokin rayuwarsa na yau da kullum.

Yanzu haka dai, shugabannin Afrika guda uku dake cikin kwamitin raya wannan sabon shiri, watau Olusegun Obasanjo na Nijeriya, da Abdoulaye Wade na Senegal, da kuma takwaransu Abdul-aziz Bouteflika na Aljeriya, suna halartar wannan taro da ake yi a birnin Paris.

XS
SM
MD
LG