Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Madagascar Ya Ce ya Kawo Wuya - 2002-02-08


Shugaba Didier Ratsiraka na Madagascar ya shaidawa ’yan jaridun kasashen waje dake ziyara a kasar cewa yanzu kam ya kawo har wuya da zanga-zangar ’yan adawar dake ci gaba da gudana a titunan babban birnin kasar.

Shugaba Ratsiraka ya ce rashin tunani ga wani ya ce zai dakatar da gudanar al’amura a kasa baki daya kamar yadda madugun ’yan adawa, Marc Ravalomanana, yayi.

Yau aka shiga rana ta 12 da yajin aikin da ’yan adawa suka kira domin jaddada bukatunsu cewar Mr. Ravalomanana shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan Disamba kai tsaye.

A halin da ake ciki dai, wasu magoya bayan shugaban kasar su kimanin 50 sun toshe wata hanyar motar dake tsakanin babban birnin kasar da kuma daya daga cikin muhimman tasoshin jiragen ruwan wannan tsibiri domin su nuna rashin jin dadinsu da wannan zanga-zanga da ’yan adawa keyi.

XS
SM
MD
LG