Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Rikon Afghanistan Ta Sako Mayakan Taleban 350 - 2002-02-09


A wani matakin neman sasantawa yayin da take maida hankali kan sake gina kasar da yaki ya lalata, gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan ta sako daruruwan tsoffin mayakan Taleban.

A lokacin da yake magana ga fursunoni 350 wadanda suka yi layi suna makyarkyata saboda sanyin hunturu a gaban fadar shugaban kasa yau asabar a Kabul, jagoran gwamnatin rikon kwarya, Hamid Karzai, ya bukaci mutanen da su koma gidajensu a tsohuwar tungar 'yan Taleban a kudancin Afghanistan. Ya bukace su da su nemi aikin yi maimakon daukar bindigogi.

Mr. Karzai bai bayyana yadda aka kama wadannan mutanen ba, amma ya bayyana su a zaman wadanda aka sanya aikin soja ala tilas. Hukumomi sun sallami kowane fursuna da guzurin Afghani dubu 500 a kudin kasar, kimanin Dalar Amurka 15.

A halin ad ake ciki, sojojin Amurka a Afghanistan suna yin tambayoyi wa tsohon jami'in Taleban mafi girma da aka san cewa an kama ya zuwa yanzu, watau tsohon ministan harkokin waje Wakil Ahmad Muttawakil.

Hukumomi suna fatan samun bayanan da zasu taimaka musu wajen farautar shugaban Taleban, Mullah Mohammad Umar, da sauran kusoshin kungiyar.

XS
SM
MD
LG