Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tony Blair yayi Alkawarin Taimakawa Saliyo - 2002-02-09


Firayim minista Tony Blair na Britaniya yayi alkawarin bada tallafin sake gina kasa ga Saliyo, yayin da kasar ke gwagwarmayar sake farfadowa a bayan yakin basasar shekaru 10.

A lokacin da ya yada zango yau asabar a ci gaba da ziyarar da yake yi a wasu kasashe 4 na Afirka ta Yamma, Mr. Blair yayi jawabi ga mutanen da suka taru a filin jirgin saman dake wajen Freetown, babban birnin kasar. Ya yabawa sojojin Britaniya, wadanda suka shafe shekaru biyu a Saliyo suna tallafawa sojojin gwamnati da dakarun kiyaye zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Har ila yau Mr Blair yayi alkawarin cewa Britaniya zata ci gaba da tallafawa Saliyo. Ya ce yana da muhimmanci ga kasashen duniya su yi kokarin sake gina kasar, kamar yadda suka taimaka wajen kawo karshen yakin basasar da aka yi a can. A watan da ya shige aka ayyana karshen yakin basasa mai munin gaske da aka yi shekaru goma ana yi a Saliyo, a bayan da aka kawo karshen shirin da MDD ta gudanar na kwance damarar yaki.

A lokacin wannan ziyara tasa ta kimanin sa'o'i uku, Mr. Blair ya gana da shugaba Ahmed Tejan Kabbah, da wakilin MDD na musamman, Oluyemi Adeniji. Daga nan firayim ministan ya tashi zuwa Senegal, zangonsa na karshe a wannan ziyara.

A jiya Jumma'a Mr. Blair yayi jawabi gaban majalisar dokokin Ghana. Shi ne firayim ministan Britaniya na farko da ya ziyarci Ghana, kasar da Britaniya tayi wa mulkin mallaka, a cikin shekaru fiye da 40.

XS
SM
MD
LG