Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Pakistan Sun Damke Wanda Ake Zargi Da Laifin Sace Dan Jarida - 2002-02-12


'Yan sandan Pakistan sun ce sun damke babban mutumin da ake tuhuma da laifin sace Ba'Amurke dan jarida Daniel Pearl fiye da makonni biyun da suka shige.

'Yan sanda sun ce yau talata aka kama Ahmed Omar Saeed Sheikh, malami haifaffen kasar Britaniya, a birnin Lahore, hedkwatar lardin Punjab a gabashin Pakistan.

Sanarwar kama Sheikh Omar ta zo ana saura kwana guda kafin shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya gana da shugaba Bush a nan birnin Washington.

Har yanzu babu wani bayanin da aka samu dangane da makomar Mr. Pearl, ma'aikacin jaridar Wall Street Journal, wanda ya bace a birnin Karachi dake kudancin Pakistan a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta yin hira da wani malamin addinin Islama.

Tun da fari a yau talata, wata kotun yaki da ta'addanci a Karachi, ta bada umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane uku wadanda ake zargi da laifin aikewa da sakonnin sace Mr. Pearl ta cikin Kwamputa.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kama wasu mutanen da dama a biranen Karachi da Rawalpindi, da wasu biranen.

XS
SM
MD
LG