Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Suna Gudu Daga Liberiya - 2002-02-13


Gwamnatin Liberiya tana ci gaba da damke mutanen da take zaton magoya bayan ’yan tawaye ne a babban birnin kasar, Monrovia, bayan da ta ayyana dokar-ta-baci a makon jiya. Gwamnati da ’yan tawaye duk sun ce fada ya kara rincabewa kusa da babban birnin. Wakilin Muryar Amurka Luis Ramirez ya ce an bada rahoton dubban mutane suna ci gaba da gudu daga kasar, yayin da gwamnati ta ce daga gobe alhamis, zata bukaci duk mai son barin kasar da ya samu takardar iznin yin hakan tukuna.

Mazauna Monrovia sun ce babu tashin hankali cikin birnin, amma kuma akwai zaman dar-dar. Shaidu sun ce mutane sun yi layuka a bankuna suna karbar kudin da ’yan’uwansu dake kasashen waje suka aiko musu domin su samu sukunin gudu. Wasu suna tashi ta jiragen sama, amma akasarinsu suna gudu ne ta kasa a cikin motoci. Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta MDD ta ce wasu ’yan gudun hijiran sun tsallaka bakin iyaka suka shiga cikin saliyo, wasu kuma sun doshi Cote D’Ivoire da Ghana.

Takardar iznin barin kasa tana daya daga cikin sabbin matakan da gwamnatin shugaba Charles taylor ta dauka karkashin dokar-ta-bacin da shugaban ya ayyana ranar jumma’a, bayan da aka samu rahotannin cewa ’yan tawaye sun kama garin Klay, mai tazarar kilomita 40 kawai daga birnin Monrovia. Gwamnati ta ce a yanzu garin yana hannun dakarunta.

A cikin wannan mako ma’aikatar yada labarai ta Liberiya ta umurci dukkan kungiyoyi da ’yan jarida kan cewa kada suyi sharhi kan dokar-ta-bacin da aka kafa har sai sun samu izni daga hukumomi. ‘Yan sanda sun kama ’yan jarida uku ranar talata, a bayan da jaridarsu mai suna “Analyst” ta Monrovia ta buga rahotannin dake kalubalantar shawarar shugaba Taylor ta kafa dokar-ta-baci. An sako su da maraicen talatar a bayan da ’yan sanda suka yi musu tambayoyi na tsawon sa’o’i.

Hukumomin Liberiya sun ce za a ci gaba da kama mutane a wani bangare na kokarin zakulo magoya bayan ’yan tawaye wadanda gwamnati take kira ’yan ta’adda.

Yau kusan shekaru biyu ke nan ’yan tawaye na wata kungiya da ake kira, a Hausance "Gamayyar ’yan Liberiya Masu Neman Sake Gina Kasa da Kafa Mulkin Dimokuradiyya," take kokarin hambarar da shugaba Charles Taylor daga kan karagar mulki. Gwamnatin Mr. Taylor tana zargin Guinea, makwabciyarsu, da laifin goyon bayan kungiyar ’yan tawayen, zargin da ita kuma Guinea ta musanta.

XS
SM
MD
LG