Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaman Sauraron Daukaka Karar Dan Libya a Netherlands - 2002-02-13


Wata kotun daukaka kara a kasar Netherlands ta fara sauraron shaidar da zata iya sanyawa a soke hukumcin samun wani dan kasar Libya da laifin dana bam a jirgin saman kamfanin Pan Am wanda ya tarwatse a samaniyar Scotland a 1988. Wannan fashewa tayi sanadin mutuwar dukkan mutane 259 dake cikin jirgin da kuma wasu mutane 11 a kasa.

Wakilin Muryar Amurka a Luxembourg, Douglas Bakshian ya ce alkalan wannan kotu sun saurari shaida na farko daga cikin sabbin shaidun da lauyoyin kariya suka gabatar. Raymond Manly, wani mai gadi a filin jiragen saman Heathrow a birnin London, ya bada shaidar cewa a ranar da wannan jirgin na Pan Am dake kan hanyar zuwa New York zai tashi a 1988, ya zo ya ga alamar cewa an fasa inda ake tara akwatuna da sauran kayayyakin da za a sanya a cikin jirgin.

A makon da ya shige lauyoyin kariya suka shaidawa kotun daukaka karar cewa shaidar da Mr. manly zai gabatar zata goyi bayan ikirarin da suka yi cewa a bisa dukkan alamu a birnin London ne aka shigar da jakar dake kunshe da bam cikin wannan jirgi, maimakon a kasar Malta kamar yadda masu gabatar da kara suka ce. Shi ma shugaban masu gadi a filin jirgin saman na Heathrow a lokacin, ya bada shaida inda ya ce lallai a wannan rana Mr. Manly ya ba shi labarin cewa an fasa wurin tara kayayyakin aka shiga.

Ba a kira jami’an tsaron filin jirgin saman suka bada shaida a lokacin shari’ar farko da aka yi ba, kuma lauyoyin dake kariya sun ce sam ba su da masaniya game da wannan batu na fasawa da shiga wurin tara kayan har sai bayan da aka yanke hukumci kan shari’ar farko a bara.

Kotun da tayi shari’ar ta samu tsohon jami’in leken asirin Libya Abdel Basset Ali Al-Megrahi da laifin sanya jaka dauke da bam a wurin tara kayayyakin da za a saka cikin jirgin a filin jirgin saman kasar Malta, inda daga baya aka dauki wannan jaka aka sanya cikin jirgin saman kamfanin Pan Am mai lambar tafiya 103. An same shi da laifi aka yanke masa hukumcin daurin rai da rai.

Shari’ar farko tafi dogara ne kan shaidar da wani mai kanti a kasar Malta ya bayar cewa al-Megrahi ya sayi tufa a kantinsa, tufar da daga bisani ’yan sanda suka ce ita ce aka yi amfani da ita wajen kunshe bam cikin wannan jaka.

Lauyoyin kariya suna kokarin tuhumar sahihancin shaidar da mai kantin ya bayar tare da nuna sabani ko rashin alaka tsakanin abinda ya faru da shaidar da aka bayar. Masu gabatar da kara sun ce shaidar da suka bayar kan al-Megrahi, koda yake ba ta kai tsaye ce ba, har yanzu tana da karfi.

Wata kotun daukaka kara ta musamman ta Scotland ce take sauraron wannan kara a wani tsohon sansanin soja da ake kira Camp Zeist a Netherlands.

XS
SM
MD
LG