Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bafalasdine Ya zamo Sabon Jami'in Gudanarwa Na Al-Qa'ida - 2002-02-15


Jaridar New York Times ta ce wani Bafalasdine mai shekaru 30 da haihuwa ya zamo sabon babban jami’in gudanar da ayyuka na kungiyar al-Qa’ida, an kuma yi imanin cewa yana shirya hare-haren da tuni aka tsara, amma ba a aiwatar ba, a kan Amurka.

Jaridar ta New York Times ta ambaci wasu jami’an Amurka da ba a fadi sunayensu ba suna fadin cewa an alakanta hannun Abu Zubaida kai tsaye a shirya hare-haren ranar 11 ga watan Satumba, da kuma shirye-shiryen wasu hare-haren da aka shirya kaiwa a nahiyar Turai cikin shekarar da ta shige.

Jaridar New York Times ta ce masu bincike na Amurka sun yi imanin cewa a yanzu Abu Zubaida yana kokarin farfado da gungu-gungun ’yan al-Qa’ida wadanda suka yi kwanton bauna cikin wasu kasashe, domin kai sabbin hare-hare kan Amurka da kawayenta.

XS
SM
MD
LG