Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya gana da Firayim Minista Koizumi - 2002-02-18


Shugaba Bush ya bayyana kwarin guiwa sosai cewar firayim ministan Japan, Junichiro Koizumi, yana tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar ta hanyar da ta fi dacewa, ya kuma godewa Japan saboda goyon bayan da take bayarwa a yaki da ta’addanci.

A wajen taron ’yan jarida na hadin guiwa da suka yi bayan sun tattauna yau litinin a Tokyo, Mr. Bush ya ce yana da kwarin guiwa kan dabarar da Mr. Koizumi ya bullo da ita ta farfado da tattalin arzikin Japan, ya kuma yi imanin cewa zai iya aiwatar da ita.

Mr. Bush ya bayyana kawancen Amurka da Japan a zaman ginshikin tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki a yankin tekun Pacific, yana mai fadin cewa yana da muhimmanci ga kasa ta biyu wajen karfin tattalin arziki a duniya ta bunkasa.

Mr. Koizumi ya shaidawa ’yan jarida cewa zai dauki dukkan matakan da zasu yiwu domin takalar karyewar darajar kayayyaki tare da fuskantar matsalar karancin kudi. Ya bayyana furucin Mr. Bush na bayyana wasu kasashe uku da cewar suna da mummunar akidar mugunta, a zaman alamar kudurin Amurka na yaki da ta’addanci.

Mr. Bush ya ce yana son ya warware sabanin dake tsakaninsu da Iran da Iraqi da kuma Koriya ta arewa cikin lumana. Wadannan kasashe uku sune Mr. Bush ya bayyana a zaman masu akidar mugunta. Sai dai kuma ya kara da cewa za a iya daukar kowane irin mataki wajen magance wannan.

XS
SM
MD
LG