Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nepal Ta Lashi Takobin Daukar Wasu Matakai, Tsaurara, Kan'Yan Tawaye - 2002-02-18


Jami‘an tsaro a NEPAL suna zaune cikin shiri bayan da gwamnatin kasar ta lashi takobin daukar mataki mai tsauri a kan ’yan tawayen Maoist wadanda suka kai kazaman hare-haren da ba‘a taba ganin irinsu ba a mulukiyar dake yankin na Himalaya.

Mayakan ’yan tawayen sun kashe akalla mutane dari da Talatin da uku a hare-haren da suka fara kaiwa tun daga daren Asabar da ta gabata a lardin Accham dake Yammaci.

Mafi yawan wadanda suka galabaita ’yan sanda ne da soja. Hukumomin Nepal sun bayyana cewa mayakan ’yan tawayen su ma sun jikkata sosai.

Gwamnatin Nepal ta tura karin soja zuwa kuryar yankunan kasar domin farautar ’yan tawayen. Majalisar dokokin kasar wani lokaci a wannan makon ake kyautata cewar zata kada kuri‘a kan daftarin dokar fadada aiki da dokar-ta-bacin da Gwamnati ta kafa tun watan Nuwamban da ya gabata bayan wargajewar tattaunawar neman zaman lafiya tare da ’yan tawayen.

XS
SM
MD
LG