Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Tawayen Fiji Ya Tsallake Rijiya Da Baya - 2002-02-18


A yau shugaba Josefa Iloilo na Fiji ya soke hukumcin kisan da aka yankewa madugun juyin mulki, George Speight, ya maida shi daurin rai da rai.

shugaba Iloilo ya rattaba hannu kan dokar sauya hukumcin jim kadan a bayan da kotun kolin kasar ta bada umurnin zartas da hukumcin kisa kan Mr. Speight.

Mr. Speight ya jagoranci tawayen da ya hambarar da gwamnatin tsibirin Fiji a cikin watan Mayun shekarar dubu biyu. An yankewa Mr. Speight hukumcin kisa bayan da ya amsa laifin cin amanar kasa a shari'ar da akayi masa a Suva, babban birnin tsibirin Fiji dake kudanci tekun Pacifica. Alkalin da yayi shari’ar ya nemi da a rataye Mr. Speight.

XS
SM
MD
LG