Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafawa Zimbabwe Takaitaccen Takunkumi - 2002-02-18


Kungiyar Tarayyar Turai, KTT, ta yanke shawarar kakabawa Zimbabwe takunkumi a wasu kayyadaddun fannoni, zata kuma janye ’yan kallon zabenta daga kasar.

Ministocin harkokin wajen KTT dake ganawa a birnin Brussels sune suka bayyana wannan matakin yau litinin, a bayan da suka ji ta bakin babban jami’in kallon zabe na kungiyar, Pierre Schori, wanda aka kora daga Zimbabwe ranar asabar.

Wannan takunkumin zai shafi shugaba Robert Mugabe ne kawai da wasu mukarrabansa su 19. Shugabannin KTT sun ce wadanda ke cikin jerin sunayen ba zasu iya yin tafiya zuwa cikin wata kasa ta kungiyar ba, haka kuma duk wata dukiya ko kadara da suke da ita a can za a garkame.

Jami’an kungiyar sun jaddada cewa za a ci gaba da bada agajin jinkai, kuma an kafa wannan takunkumin ne kawai a kan mutanen da ake jin cewa sune suke take hakkokin jama’a kafin zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai zuwa.

Zimbabwe ta ki yarda da wasu daga cikin ’yan kallon KTT tana mai cewa suna nuna tsana ga gwamnatin kasar. Yau litinin a birnin Harare, magoya bayan shugaba Mugabe sun jefa duwatsu kan hedkwatar jam’iyyar hamayya ta MDC

XS
SM
MD
LG