Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kazamin Fadan Kabilanci a Kwango Kinshasa Ya Kashe Mutane Fiye Da 100 - 2002-02-18


Uganda ta tura sojoji domin su kwantar da wutar rigimar kabilanci a yankunan da suke karkashin ikonta a Jamhuriyar Dimokuradiyya ta Kwango, watau Kwango Kinshasa.

Majiyoyin sojan Uganda sun ce an kashe kauyawa su akalla 100 cikin ’yan kwanakin nan, a lokacin da aka gwabza tsakanin kabilun Lendu da Hema, wadanda ke gaba da juna a arewa da garin Bunia na arewacin Kwango. Kabilun biyu sun jima suna fada da junansu kan yin amfani da wasu filaye.

A bisa al’ada, kabilun sukan yi amfani da kwari da baka da kuma adduna, amma fadan ya kara yin muni cikin ’yan kwanakin nan a saboda yaduwar bindigogi da makaman zamani a wannan kasa.

Wannan yanki dai yana hannun ’yan tawaye masu samun goyon bayan Uganda.

Uganda ta janye wasu daga cikin sojojinta dake wannan yanki a wani yunkurin kawo karshen yakin basasar Kwango. Amma kuma irin wannan tashin hankali na kabilanci yana barazanar gurgunta kokarin da ake yi na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tare da tabbatar da janyewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar.

XS
SM
MD
LG