Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun kashe Falasdinawa Tara - 2002-02-19


A ci gaba da tashe-tashen hankulan dake bazuwa a yankin gabas ta tsakiya, sojojin Isra‘ila sun kashe ’yan Falasdinu akalla tara, a wani matakin maida martani ga hare-haren da falasdinawan suka kai har suka kashe Yahudawan Isra‘ila hudu.

Wani jirgin saman yakin Isra‘ila mai sauka da tashin ungulu ya harba roka a kan ginin ofishin kungiyar jihadin Hamas dake cibiyar ’yan gudun hijirar Falasdinu ta Jabalya a Zirin Gaza, har ma sun kashe mutane biyu.

A safiyar yau, jami‘an Falasdinu sun bayyana cewa an kashe mutane uku a garin Khan Yunis lokacin da tankokin Isra‘ila suka rurrusa gidajen Falasdinawa masu yawan gaske. Sannan jiragen saman yakin Isra‘ila sun kai hare-haren boma-bomai a wata cibiyar ayyukan tsaron Falasdinawa dake Zirin Gaza, inda sojan Isra‘ila suka harbe wasu ‘yan Falasdinu biyu suka mutu har lahira a kusa da wani yankin kama wuri zaunan yahudawa.

A can Yammacin Kogin Jordan kuma, jiragen saman yakin Isra‘ila samfurin F-16 sun kai wasu hare-haren a kan hedkwatar hukumar cin gashin kan Falasdinawa dake kusa da Ramallah, sannan sojojin Isra‘ila sun kashe wasu ’yan falasdinu dake dauke da makamai a wani karon battar da suka yi a kusa da sansanin ’yan gudun hijira dake dab da Batala a Nablus.

XS
SM
MD
LG