Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Kwango Kinshasa Zasu Janye Daga Shawarwari - 2002-02-19


Wani babban madugun 'yan tawaye a Jamhuriyar Dimokuradiyya ta Kwango, watau Kwango Kinshasa, ya ce kungiyarsa zata janye daga shawarwarin neman zaman lafiyar da aka shirya gudanarwa a kasar Afirka ta Kudu cikin mako mai zuwa, matakin da ya kawar da kwarin guiwar cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki a kasar.

Shugaban kungiyar 'yan tawaye ta "Congolese Liberation Movement", Jean Pierre Bemba, ya shaidawa taron 'yan jarida yau talata a birnin Paris cewa abin takaici ne ganin yadda taron neman zaman lafiyar ya wargaje tun ma kafin a gudanar da shi.

Mr. Bemba ya ce kungiyarsa ta yanke shawarar cewa ba zata halarci taron ba saboda ba za a wakilci kungiyoyin siyasa na 'yan hamayya kamar yadda ya kamata a zauren taron ba. Ya ce akasarin kungiyoyin siyasar dake shirin halartar taron sanannun kawayen gwamnatin Kwango Kinshasa ne.

Kungiyar Mr. Bemba tana daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yan tawaye biyu a Kwango. An shirya fara tattaunawa ranar litinin 25 ga watan nan na Fabrairu a gandun shakatawa na Sun City dake Afirka ta Kudu domin shirya yadda za a aiwatar da tsarin siyasa a Kwango Kinshasa, kamar yadda aka yi tanadi cikin yarjejeniyar zaman lafiyar 1999, wadda take tangal-tangal.

XS
SM
MD
LG