Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kiyaye Zaman Lafiyar Britaniya Da Suka Yi Harbi Kan Wata Mota a Kabul Sun Koma Gida - 2002-02-19


Wasu sojojin kiyaye zaman lafiya biyu na Britaniya, wadanda aka yi zargin cewa sun yi harbi kan wata motar dake dauke da wata mace mai juna biyu, sun koma gida yayin da ake zarge-zargen cewa sun yi wannan harbi ne ba tare da an tsokane su ba.

An kashe dan’uwan mijin wannan mata a lokacin harbin.

Wani kakakin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiyar Britaniya, ya ce ’yan sandan Afghanistan da na Britaniya suna binciken wannan lamari, amma kuma sojojin zasu amsa tambayoyin ’yan sandan Britaniya ne kawai.

Wannan lamari da ya faru cikin dare a makon jiya a birnin kabul, ya harzuka ’yan Afghanistan wadanda suka ce sojojin sun yi harbi ba tare da tsokana ba a kan motar da ta dauko wannan mata mai ciki zata garzaya da ita zuwa asibiti, koda yake a lokacin akwai dokar hana yawon dare.

XS
SM
MD
LG