Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Charles Taylor Ya Ce Nan Bada Jimawa ba Zai Gana da Shugabannin Saliyo da Gini - 2002-02-19


Shugaba Charles Taylor na Laberiya ya ce nan ba da jimawa ba a kasar Maroko zai gana da shugabannin kasashen Guinea da Saliyo masu makwabtansa domin su tattauna akan boren dake gudana a ketaren kan iyakokinsu.

Mr.Taylor ya ce Sarkin kasar Maroko, Mohamed na Shidda, ya gayyaci shugabannin kasashen ukku na Afirka ta yamma, su halarci taron kolin da za’a yi a kasar, amma bai yi wani karin bayani ba. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce za’a yi taron kolin ne a ranar 27 ga watan nan na Fabrairu idan Allah Ya kai mu.

Kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo su na zargin junan su akai-akai da goyon bayan ’yan tawaye a cikin kasashensu.

Da farkon wannan wata, shugaba Taylor ya ayyana dokar-ta-baci domin magance wani bore na ’yan tawayen kasar. Gwamnatin Laberiya ta zargi kasar Guinea da tallafawa ’yan tawayen. Tun shekarar 1999 ’yan tawayen suke fafatawa da dakarun gwamnatin Charles Taylor a arewacin kasar, amma sai a ’yan kwanakin nan kawai ne suka kusanci Monrovia, babban birnin kasar.

A halin yanzu dai wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya ce ana bukatar kara yin kokari domin taimakawa dubban daruruwan mutanen da yakin na Laberiya ya warwatsa. Karamin darektan hukumar MDD mai kula da agajin gaggawa, Ross Mountain, ya yi kiran neman taimakon kasa-da-kasa a karshen wata ziyarar aikin kwanaki ukku da ya kai Laberiya. Mr.Mountain ya ce al’amarin mutanen da suka shiga tsaka mai wuya saboda yaki, ya na da muni, kuma mai tsanani ne kwarai da gaske.

XS
SM
MD
LG