Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali Yayi Tsanani a Gabas ta Tsakiya - 2002-02-20


Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 15 a hare-haren ramuwar gayya, a bayan da aka yi kwanton-bauna aka hallaka sojojin Bani Isra’ila 6 a daya daga cikin barna mafi muni da aka taba yiwa sojojin Isra’ila tun lokacin da Falasdinawa suka fara tunzuri watanni 17 da suka shige.

Wata kungiyar ’yan kishin Falasdinu mai suna “Birged Din ’Yan Shuhada’u na Masallacin al-Aqsa” mai alaka da kungiyar Fatah ta Mallam Yasser Arafat ta dauki alhakin kashe sojojin jiya talata a wani wurin da sojoji suka kafa shinge a yankin yammacin kogin Jordan suna binciken ababen hawa.

Domin daukar fansar wannan hari, sojojin Isra’ila sun kaddamar da hare-hare ta kasa, ta ruwa, da kuma ta sama a kan cibiyoyin Falasdinawa a zirin Gaza da yankin yammacin kogin Jordan. An kashe zaratan dogarawan Malam Arafat da ake kira Force-17 su hudu a Gaza. A garin Nablus na yankin yammacin kogin Jordan, sojojin Bani Isra’ila sun kashe Falasdinawa 9 cikinsu har da ’yan sanda 6, yayin da suka kashe wasu Falasdinawan guda biyu a Ramallah da wani kauyen dake kusa da nan.

Rundunar sojojin Isra’ila ta ce ta rufe hanyoyin mota ta kuma haramtawa Falasdinawa yin tafiye-tafiye a tsakanin birane da kauyukan yankin yammacin kogin Jordan.

Firayim ministan Isra’ila Ariel Sharon ya gana da manyan ministocinsa domin tattauna ci gaba da zub da jinin. Wata sanarwa daga ofishin Mr. sharon ta ce firayim ministan ya yanke shawarar daukar wani matakin na dabam a kan ’yan kishin Falasdinu. Sanarwar ba ta yi karin bayani ba.

Wani mukarrabin Mallam Arafat, Ahmed Abdul-Rahman, ya ce hare-haren sojan na Isra’ila wani sabon laifi ne, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen abinda ya kira cin zarafi da nuna fin karfin da Isra’ila ke yi.

XS
SM
MD
LG