Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahajjata Sun Yi Hawan Arafat - 2002-02-21


Mahajjata miliyan biyu daga kasashen duniya dabam dabam a yau sukayi hawan Arafa yayin aikin Hajjin bana a can Makka, Saudiya. Majajjata sunyi tsayuwa daidai inda Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yayi hudubar karshe.

Babban limamin Makka, Mufti Abdul-aziz-al-Sheik, yayi hudubar cewa ba abinda ya hada musulunci da ta’addanci, yayin da yayi kira ga musulmi da su haa kai tare kuma da nuna goyon baya ga Falasdinawa.

Alhazan kasar Iran sunyi zanga zangar nuna rashin goyon bayan Amurika da Israila, kamar yadda suka saba yi a kowace shekara, duk da kuwa gargadin gwamnatin Saudiya na kada a gudanar da wata zanga zanga dake da nasaba da siyasa.

Mahajjata a wajen Arafa sunyi addu'a tun safe har zuwa faduwar rana, daga bisani suka wuce Muzdalifa inda zasu wuce da duwatsu wajen jifan shedan a gobe juma’a.

XS
SM
MD
LG