Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tabbatar Da Mutuwar Amurkawa Uku a Philippines - 2002-02-22


An tabbatar da mutuwar Amurkawa uku, yayin da har yanzu ba a san makomar guda 7 ba, a bayan da wani jirgin saman yaki mai saukar ungulu na zaratan sojojin Amurka ya fadi a yankin kudancin kasar Philippines.

Wani babban jami’in rundunar zaratan sojojin Amurka ya fada a yau Jumma’a cewa har yanzu ba a samu wani da rai ba a inda jirgin ya fadi, amma kuma ana iya bakin kokari domin gano wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

Tun da fari, jami’an Philippines sun ce masunta sun ceto mutane biyu ko uku da ransu a bayan faduwar jirgin, amma kuma jami’an Amurka sun ce wannan rahoto ba gaskiya ba ne.

Jirgin na sojan Amurka ya fadi a kusa da tsibirin Basilan. Zaratan sojojin na Amurka suna gudanar da aikin horaswa a can, inda suke taimakawa sojojin gwamnatin Philippines wajen yakar ’yan sari-ka-noken kungiyar Abu Sayyaf, wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyar ’yan ta’adda ta al-Qa’ida.

XS
SM
MD
LG