Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye a Nepal Sun Kashe Mutane 41 - 2002-02-22


‘Yan tawayen Moist a kasar NEPAL sun kashe mutane arba‘in da daya, mafi yawansu ’yan sanda a lardin yammacin kasar. Sun gudanar da kashe-kashen ne a lokacin da suka shammaci wani ofishin ’yan sandan dake can cikin kurya, wanda nisansa ya kai kilomita metan da sittin yamma da babban birnin kasar, Kathmandu.

Wasu mutane biyar sun mutu a lokacin da ’yan tawayen suka kai harinsu na biyu a wani lardin, inda ’yan tawayen suka jefa boma-boman fetur a kan wata safa.

A jiya Alhamis, majalisar dokokin kasar ta kada kuri‘ar amincewa da fadada lokacin aiki da dokar ta bacin da Gwamnati ta kafa tun watan Nuwamban da ya gabata, lokacin da ’yan tawayen, ba zato ba tsammani, suka fice daga zauren tattaunawar neman zaman lafiya sannan suka koma ga tashe-tashen hankulan jama’a.

A yau Juma‘a wani bom ya tashi a Kathmandu har wani mutum guda ya jikkata.

Mafi yawan kantunan cinikayya duk an rufesu bayan da ’yan tawayen suka bada sanarwar yin yajin aikin gama gari a duk fadin kasar domin bikin cika shekaru shida da fara tada kayar baya.

XS
SM
MD
LG