Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Daniel Pearl - 2002-02-22


An bada rahoton cewar an kashe dan jaridar nan na Amurka, Daniel Pearl, wanda aka sace a kasar Pakistan a watan da ya gabata. An ji cewa saida ’yan ta‘addar suka dauki hoton bidiyon yadda suka yanka makogwaronsa da wuka kafin ya mutu.

Shugaba Bush yace kisan da aka yiwa wakilin jaridar cinikayya ta "The wall Street Journal" aiki ne na ’yan ta’adda, kuma Amerikawa na fushi da bakin ciki da afkuwarsa.

A yau a birnin Beijing na China aka ji Mr. Bush yana cewa hanyar da aka bi wajen kashe dan jaridar na Amirka, babu abinda ta haifar illa tana karfafa matakin da Amurka ta dauka na ganin an kakkabe kurar ’yan ta‘adda a kowane sashe na duniya.

Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan yace jami‘an tsaron gwamnatinsa zasu ci gaba da farautar inda duk ’yan ta’addar suka boye.

XS
SM
MD
LG