Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Angola Yayi Kiran Tsagaita Wuta a Bayan Mutuwar Shugaban UNITA - 2002-02-25


Shugaba Jose Eduardo Dos Santos na Angola yayi kiran da a tsagaita wuta da 'yan tawayen UNITA, a bayan mutuwar madugun 'yan tawayen, Jonas Savimbi, wanda aka kashe ranar Jumma'a a wata gwabzawa da sojojin gwamnati.

Mr. Dos Santos ya shaidawa 'yan jarida yau litinin, lokacin wata ziyara a Portugal, cewar yana son ya dauki matakan gaggawa domin daidaita harkokin siyasa a kasar Angola. Ya ce za a fara wannan ta hanyar daukan matakan gaggawa na kulla tsagaita wuta.

Har ila yau shugaban na Angola ya ce yana sa ran gudanar da zabe a cikin shekaru biyu, amma ya ce wannan zai dogara ne kan cimma tsagaita wuta tare da kwance damarar yaki na UNITA.

Amma kuma 'yan tawayen na UNITA sun ce za su ci gaba da yakar gwamnati.

Wani wakilin UNITA, Carlos Morgado, ya fada ranar lahadi cewar koda yake kungiyarsa ta girgiza da mutuwar Mr. Savimbi, wannan ba ya nufin cewa zasu mika wuya a fagen daga.

Ana kyautata zaton cewa mutuwar Mr. Savimbi zata haddasa gwagwarmayar neman shugabancin kungiyar UNITA a tsakanin manyan mukarrabansa biyu, Antonio Dembo da Paulo Lukamba Gato.

A gobe talata ake sa ran cewa shugaba Dos Santos na Angola tare da shugabannin Mozambique da Botswana, zasu gana da shugaba Bush na Amurka a fadar White House.

An shirya ganawar tasu tun kafin mutuwar Mr. Savimbi, domin tattauna kwanciyar hankalin siyasa ad tsaro a yankin kudancin Afirka, da bunkasa harkokin cinikayya da raya kasa, da yaki da talauci da kuma cutar AIDS.

XS
SM
MD
LG