Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankokin Isra'ila Sun Janye Daga Hedkwatar Malam Arafat - 2002-02-25


Rundunar sojojin kasar bani-Isra'ila ta daina yin kawanyar data dade tana yi wa hedkwatar Yasser Arafat a Ramallah, to amma kuma har yanzu sun ci gaba da hana shugaban na Palasdinawa yin tafiya ko barin wannan birni dake yammacin kogin Jordan.

Yau (litinin) da jijjifi ne tankokin yakin Isra'ila suka janye, bayan da majalisar harkokin tsaron Firayim minista Ariel Sharon ta yanke shawarar sassauta irin matsanancin takunkumin da suka yi wa Malam Arafat a jiya lahadi. Tun a farkon watan Disemba ne Isra'ila ta hana Malam Arafat barin hedkwatar tasa, inda ta nemi sai lallai ya kame, tare da mika mata mutanen da suka kashe ministan yawon-shakatawar Isra'ila, wanda aka bindige a cikin watan Oktoban da ya gabata.

Yanzu majalisar harkokin tsaron ta Isra'ila ta ce zata duba duk wata bukatar da Malam Arafat ya mika mata, ta son yin tafiya zuwa wajen birnin na Ramallah.

Jami'an Palasdinawa sun ce Malam Arafat yana fatan zai samu zarafin zuwa taron kolin shugabannin kasashen larabawan da za a yi a birnin Beirut a cikin watan gobe. Babban jami'in kula da diflomasiyya na tarayyar turai, Javier Solana, ya ce, ya kamata a baiwa Malam Arafat cikakken 'yancin yin zurga-zurga domin ya samu razafin yin ayyukansa.

Bayan wata ganawar da ya yi yau da ministan harkokin wajen Isra'ila, Shimon Perez, a birnin Qudus, Mr. Solana ya shedawa manema labarai cewa kul-ba-jima-kul-ba-dade baiwa shugaban na palasdinawa sukunin yin tafiye-tafiye shine abu mafi alheri.

Jami'in na tarayyar turai ya isa yankin ne a jiya lahadi da maraice kuma an shirya zai gudanar da jerin tarurruka da jami'an Isra'ila da na palasdinawa a wani kokari na kawo karshen taho-mu-gamar da Isra'ila da palasdinawa suka yi watanni 17 suna yi.

A halin da ake ciki kuma, Mr. Perez ya nemi gafarar kakakin majalisar dokokin mulkin kan Palasdinawa, Ahmed Qureia, bayan da sojojin Isra'ila suka bude-wuta akan motarsa a jiya lahadi da maraice a lokacin data nufi wani wurin duba matafiya da abubuwan hawan da Isra'ila ta kafa a kusa da birnin Ramallah.

Jami'an Palasdinawa sun ce an harbi motar sau da yawa, to amma babu mahalukin da ya samu koda rauni. Suka ce sojojin na Isra'ila sun bude-wuta ne akan motar a lokacin data isa wurin duba motocin.

Wata sanarwar da rundunar sojojin Isra'ila ta bayar ta ce wannan mota da ba a gane ta ba, tana yin wawan-gudu ne, al'amarin da ya sanya sojojin suka yi fargabar ko tana so ta kade su ne.

To amma mukarraban Mr. Qureia, sun ce an sanar da gwamnatin Isra'ila cewa kakakin zai yi wannan tafiya.

An ci gaba da fafata fada yau litinin a lokacin da sojojin Isra'ila suka kashe wasu palasdinawa biyu a wasu harbe-harbe dabam-dabam a yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG