Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Sammacin Madugun Hamayyar Zimbabwe - 2002-02-25


'Yan sanda sun sammaci shugaban 'yan adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, domin su yi masa tambayoyi game da zargin da ake yi masa na kitsa makircin yi wa shugaba Robert Mugabe kisan gilla.

Wani kakakin jam'iyyar MDC ta 'yan adawa ya ce, an umarci Mr. Tsvangirai da ya bayyana yau litinin a Harare domin ya amsa wasu 'yan tambayoyi.

Gwamnatin Zimbabwe ta ce, shugaban na 'yan adawa ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo tare da wata kungiyar tsara dabarun siyasar kasar Canada, suna shirya kashe Mr. Mugabe.

Mr. Tsvangirai ya musanta wannan zargi, yana mai cewa wani kokari ne kurum da shugaban yake yi na dakile shirin yakin neman zabensa kafin zaben da za a yi a ranakun 9 da 10 ga watan gobe na Maris.

Shugaban na 'yan adawa na Zimbabwe ya kasance babban mai kalubale ga mulkin shugaba Mugabe na shekaru 22 a kasar ta Zimbabwe.

XS
SM
MD
LG