Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Zasu Ci gaba Da Tattauna Batutuwan Tsaro - 2002-02-26


Isra'ila da Palasdinawa na shirin ci gaba tattaunawa akan matakan tsaro.

Jami'in tsaron Palasdinawa, Mohammed Dahlan, ya ce a yammacin yau talata za su yi tattaunawar a Tel Aviv tare da jami'an Amurka wadanda za su halarci taron.

Palasdinawa sun dakatar da tattaunawar ce akan tsaro a shekaran-jiya lahadi lokacin da Isra'ila ta ki yarda ta kawo karshen killacewar da ta ke yiwa shugaban Palasdinawa, Malam Yasser Arafat, a birnin Ramallah dake yammacin kogin Jordan.

Tankokin yakin Isra'ila sun janye daga ofishin Malam Arafat, amma sun ci gaba da zama a kewayen birnin. Malam Yasser Arafat ya yarda a ci gaba da yin tattaunawar bayan wata ganawa da yayi a jiya litinin da Javier Solana, ministan harakokin wajen tarayyar turai.

A halin yanzu kuma akwai alamun dake nuna yadda Isra'ila ke dada sha’awar wata shawarar kasar Sa'udiyya ta yin sulhu tsakanin Israila da kasashen Larabawa. An ruwaito ministan tsaron Isra'ila, Benjamin Ben Eliezer, ya na cewa shirin da Sa'udiyya ta gabatar ya kumshi abun alheri, sannan kuma ya ce ya kamata a karfafa guiwar yin hakan. Ya ce bai kamata a yi watsi da shirin ba.

Yarima Abdullah mai jiran gadon Sa'udiyya ya mika wata shawara wadda a cikinta ya ce kasashen Larabawa za su yarda da halascin kasar Isra'ila, sannan kuma su gyara huldodinsu da ita, idan Isra'ilar ta janye daga dukkan yankunan da ta mamaye tun a shekarar 1967 a lokacin yakin yankin GTT.

XS
SM
MD
LG