Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 20 Sun Mutu A Hargitsin Addini A Jihar Gujarat Ta Indiya - 2002-02-28


Hukumomin Indiya sun ce an kashe mutane akalla 20 a yamutsin addinin da ya barke a Jihar Gujarat ta yammacin kasar. Wannan yamutsi ya barke a bayan da wasu mutanen da aka ce gungun Musulmi ne, suka kashe mutane 58, akasarinsu mabiya addinin Hindu, a cikin wani jirgin kasa da suka bankawa wuta.

Hargitsi ya barke a fadin jihar a yayin da matasa mabiya addinin Hindu suka fara jifa kan masallatai tare da kona kantunan Musulmi. Har ila yau an samu rahotannin daddatsa mutane tare da harbe wasu.

Tashin hankali mafi muni ya wakana a birnin Ahmedabad, cibiyar harkar kasuwanci ta jihar, inda sai da 'yan sanda suka fara yin harbe-harben kan-mai-uwa-da-wabi domin tarwatsa 'yan bore. An kafa dokar hana yawo baki daya a wasu sassan birnin.

Har ila yau matasa mabiya addinin Hindu, suna tilastawa jama'a mutunta yajin aikin gama gari da suka kira domin nuna rashin yarda da harin da aka kai jiya laraba kan jirgin kasa dake dauke da 'yan tsageran addinin Hindu. Wannan harin ya wakana a garin Godhra, mai tazarar kilomita 150 daga birnin Ahmedabad.

'Yan tsageran mabiya addinin Hindu suna komowa ne daga wani gangamin da suka yi a garin Ayodhya na arewacin kasar, inda masu kishin addinin Hindu suke son gina wurin ibadarsu a daidai inda 'yan gani-kashe-nin Hindu suka rushe wani Masallaci karfi da yaji a 1992.

Firayim minista Atal Behari Vajpayee ya roki mabiya addinin Hindu da kada su dauki matakan fansa, yana mai cewa tilas ne a kare 'yan'uwantakar dukkan Indiyawa ta kowane hali. Har ila yau yayi kira ga kungiyoyin mabiya addinin Hindu da kada su ci gaba da kokarin ad suke yi na gina wurin ibadarsu a wannan fili da ake takaddama kai a Ayodhya.

Amma kuma, babbar kungiyar 'yan Hindu dake jagorancin yunkurin gina wurin ibadar, "Vishwa Hindu Parisad," ko kuma Majalisar Hindu ta Duniya, ta lashi takobin fara aikin gina wurin ibadar a ranar 15 ga watan Maris, duk da umurnin da wata kotu ta bayar cewa kada kowa ya gina wani abu a wannan wuri.

XS
SM
MD
LG