Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin NATO Sun Kaddamar Da Gagarumar Farautar Neman Radovan Karadzic - 2002-02-28


Sojojin kiyaye zaman lafiyar NATO sun killace wani yanki a kudancin kasar Bosnia Herzegovina, inda aka yi amanna wata maboyar Radovan Karadzic, tsohon shugaban mayakan sa kan Sabiyawan Bosnia ne, wanda kuma ake tuhuma da aikata miyagun laifuffukan yaki.

Sai dai kuma an ce ba su same shi ba.

Wata sanarwar da NATO ta bayar ta ce sojojin sun kama wasu rumbuna uku na makamai a wani gida dake kusa da garin Foca, a kudu maso gabashin birnin sarajevo. Ta ce sojojin ba su samu Mr. Karadzic ba.

Jami’ai sun ce jiragen sama masu saukar-ungulu da motocin yaki masu sulke da tulin sojoji daga rundunar tabbatar da zaman lafiyar NATO sun killace yankin dake daf da garin Foca, a kusa da kan iyakar yankin Montenegro.

Rahotannin kafofin labaran Sabiyawan Bosnia sun baiyana cewa sojojin na NATO suna shiga ko binciken gidaje da makarantu da Majami’u da sauran gine-gine a yankin. Haka kuma an ce an katse hanyoyin sadarwar wayar Talho da Radiyo da kuma wutar lantarki a yankin.

Kotun duniya mai shari’ar laifuffukan yaki dake birnin Hague ta gabatar da tuhuma akan Mr. Karadzic, bisa zargin aikata laifuffukan yaki da kisan kare dangi a lokacin yakin da aka gwabza a Bosnia daga shekarar 1992 zuwa 1995.

Haka kuma tuhumar da ake yi masa ta hada da yi wa birnin Sarajevo kofar-raggo da kuma kisan-kiyashin da aka yi wa kimanin Musulmi dubu bakwai a garin Srebrenica a shekarar 1995.

Har yanzu akwai fiye da mutane 20 da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki, wadanda akasarinsu Sabiyawan Bosnia ne, da ba su shiga hannun hukumomi ba, a cikinsu har da Mr. Karadzic da tsohon babban hafsan sojojin Sabiyawan Bosnia, Ratko Mladic.

XS
SM
MD
LG