Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kashe Falasdinawa Akalla Goma - 2002-02-28


Sojojin Isra'ila sun kashe akalla Falasdinawa guda 10, yayin da suka jikkata wasu fiye da 90 a wasu hare-hare da suka kaiwa wasu sansanoni biyu na 'yan gudun hijira a yammacin kogin Jordan.

Sojojin na Isra'ila sun kutsa-kai ne cikin sansanin 'yan gudun hijirar Balata, da kuma wani sansanin dake Jenin, wuraren da rundunar sojin Isra'ila ta ce wasu tungogin Falasdinawa 'yan gani-kashe-ni ne.

Rahotannin dake fitowa daga kafofin Falasdinawa sun ce an kashe 'yan sanda guda 6 da wasu 'yan bindiga-dadi biyu da fararen hula 2 a yayin da ita kuma Isra'ila ta yi hasarar sojanta daya a wannan artabu.

An ce sojojin Isra'ila suna bi gida-gida a sansanin na Balata, suna sassara Bangayen gidaje suna bi ta ciki domin kaucewa fitowa kan tituna don kada 'yan bindigar Falasdinawa su harbesu.

XS
SM
MD
LG