Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Afirka ta Kudu Ya Ce Ba A Tuhumi Madugun Adawa na Zimbabwe ba - 2002-02-28


Mukaddashin shugaban kasar afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya ce gwamnatin kasar Zimbabwe ta ba shi tabbacin cewa ba a tuhumi shugaban 'yan adawar kasar, Morgan Tsvangirai, da laifin cin amanar kasar ba, kamar yadda aka bi ana yayatawa a kafofin watsa labarai.

Mr. Zuma ya yi wannan bayani ne bayan wata ziyara da ya kai da daddare zuwa kasar ta Zimbabwe domin ya tattauna da jami'an gwamnatin a ciki har da shugaba Robert Mugabe, a gabannin zaben shugaban kasar da za a yi a cikin watan gobe.

Mr. Zuma ya ruwaito gwamnatin ta Zimbabwe na cewa 'yan sanda sun yi wa Mr. Tsvangirai tambayoyi bisa zargin da aka yi masa da kitsa-makircin hallaka shugaba Mugabe, to amma har yanzu ba a gabatar da wata tuhuma akansa ba.

A ranar Litinin ne 'yan sandan Zimbabwe da shi kansa Mr. Tsvangirai, babban mai kalubalantar shugaba Mugabe a zaben na watan gobe, suka ce an tuhume shi da laifin cin amanar kasar.

XS
SM
MD
LG