Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kara Nausawa Can Cikin Wani Sansanin Falasdinawa 'Yan Gudun Hijira - 2002-03-01


Dakarun Isra'ila sun kara nausawa can cikin wani sansanin 'yan gudun hijira dake garin Jenin, wanda Falasdinawa ke mulkinsa, kwana guda a bayan da suka kaddamar ad wani farmakin soja a kan wasu sansanoni biyu na yammacin kogin Jordan.

Shaidu a garin Jenin, sun ce sojojin Isra'ila sun gwabza da 'yan bindigar Falasdinawa yau Jumma'a da safe, a yayin da sojojin suka fake da barin wutar da wasu jiragen saman kai farmaki masu saukar ungulu na Isra'ila suke yi, suka kara nausawa gaba. Jami'an Falasdinawa sun ce an kashe wani saurayi a wannan sansani, aka raunata wasu da dama.

A ranar alhamis, an kashe Falasdinawa 13 da sojan Isra'ila daya, yayin da sojojin Isra'ila dake samun taimakon tankokin yaki suka kutsa cikin Jenin da sansanin 'yan gudun hijiran Balata a kusa da garin Nablus. An raunata Falasdinawa fiye da 100. Mazauna sansanonin sun ce sojojin Isra'ila suna bi gida-gida suna farautar makamai tare da kama mutane.

Wannan shine karon farko da sojojin Isra'ila suka kutsa kai cikin sansanonin 'yan gudun hijira tun lokacin da Falasdinawa suka fara tayar da kayar baya kimanin watanni 18 da suka shige.

Isra'ila ta bayyana yankunan guda biyu a zaman makwancin 'yan ta'addar dake kai hare-hare kan 'yan Isra'ila. Ministan harkokin waje Shimon Peres ya ce sojojin na Isra'ila sun kutsa cikin sansanonin ne da nufin hanawa 'yan kunar-bakin-wake na Falasdinawa kammala ayyukansu na hare-haren bam.

Jami'an Falasdinawa suka ce Isra'ila tana kokari ne ta wargaza shawarar da Sa'udiyya ta gabatar ta maidawa da Falasdinawa yankunansu domin a samu zaman lafiya, wadda ta samu karbuwa daga kasashen duniya, ciki har da Amurka. A karkashin wannan shiri dai, kasashen Larabawa zasu kulla zaman lafiya da Isra'ila idan ta janye daga yankunan da ta mamaye a yakin Gabas ta Tsakiya na 1967.

XS
SM
MD
LG