Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Amurka Zai Doshi Sudan - 2002-03-01


Tsohon shugaban Amurka Jimmy carter, ya ce zai yi kokarin ganin an tsagaita wuta a Sudan ta yadda shi da ma'aikatan lafiya zasu samu sukunin gudanar da aikin yakar cutar kurkunu a yankin kudancin wannan kasa.

Ofishin tsohon shugaban ya fada a yau Jumma'a cewa Mr. Carter zai tattauna da jami'an gwamnati da na 'yan tawaye a lokacin ziyarar da zai kai Sudan cikin wata mai zuwa.

Wani kakaki ya ce idan ma ba a samu zaman lafiya na dindindin ba, Mr. carter yana fatan za a tsagaita wuta na tsawon lokacin da suke bukata domin gudanar da aikin yaki da cutar ta kurkunu. Mr. carter da kungiyarsa suna fatan kai ziyara zuwa kauyuka da dama a kudancin Sudan, inda fada ya fi muni a tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye.

Tsohon shugaban ya shaidawa Muryar Amurka cewa zai yi kokarin ya lallashi mutane da su ringa shan ruwan da aka tace, ko aka tafasa kawai. Ana daukar cutar kurkunu ta hanyar shan ruwan dake dauke da kananan halittu wadanda ke haddasa yaduwar tsutsotsi a cikin jikin bil Adama.

Mr. Carter ya ce an yi kusan kawar da wannan cuta baki dayanta a fadin duniya, amma kuma akwai wasu sassa, kamar kudancin Sudan, inda har yanzu cutar tana nan tana yin illa ga jama'a.

XS
SM
MD
LG