Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali Yayi Tsanani A Tsakanin Isra'ila Da Falasdinawa - 2002-03-03


Isra'ila tana nazarin karin matakan da zata dauka na mayar da martani ga hare-haren baya-bayan nan da Falasdinawa suka kai har suka kashe 'yan Isra'ila su akalla 20 daga jiya asabar zuwa yau lahadi.

Majalisar zartaswar Isra'ila ta gana yau lahadi domin tattauna wannan lamari, jim kadan a bayan da wani Bafalasdine dan bindiga shi kadai yayi kwanton-bauna ya kashe sojojin Isra'ila 7 da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna su uku a wani wurin da sojoji suka kafa shinge suna gadin wata unguwar share-ka-zauna ta yahudawa a Yankin Yammacin Kogin Jordan. An kashe wani sojan na Isra'ila lokacin wani harbi a bakin iyakar zirin Gaza.

Tankokin yaki da jiragen kai farmaki masu saukar ungulu na Bani Isra'ila sun mayar da martanin wadannan hare-haren ta hanyar kai farmaki kan cibiyoyin Falasdinawa a Yankin Yammacin Kogin Jordan. Sun kashe Falasdinawa akalla uku, cikinsu har da 'yan sanda biyu wadanda suka mutu a lokacin da Isra'ila tayi barin wuta kan garin Qalqilya. Har ila yau an kai hari kan wasu ofisoshi a kusa da hedkwatar shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a garin Ramallah.

Harbe-harben sun biyo bayan wani harin kunar-bakin-wake ranar asabar a wata unguwar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a birnin al-Qudus, inda aka kashe 'yan Isra'ila 9, aka raunata wasu 35.

Kungiyar nan da ake kira "Birged Din 'Yan Shuhada'u ta Al-Aqsa" wadda ta samo asali daga kungiyar Fatah ta Malam arafat, ta dauki alhakin kai harin. Kungiyar ta lashi takobin daukar fansar hare-haren da Isra'ila ta kai cikin makon da ya shige kan wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu a Yankin Yammacin Kogin Jordan, har ta kashe Falasdinawa fiye da 20.

Gwamnatin Isra'ila ta sha dorawa Malam Arafat laifin tarzomar da ake yi, kuma ana samun karin kiraye-kiraye a cikin Isra'ila kan a cire shi daga kan mulki.

XS
SM
MD
LG