Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Larabawa Suna Neman Hanyoyin Cimma Zaman Lafiya - 2002-03-03


Kasashen Sham (Syria) da Lebanon sun yi kiran da a samu zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar yin aiki da dukkan kudurorin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ciki har da 'yancin Falasdinawa na komawa cikin gidajensu, matakin da ba ya kunshe cikin shawarar cimma zaman lafiyar da Saudi Arabiya ta gabatar kwanakin baya.

A cikin wata sanarwar da suka bayar, shugaba Bashir al-Assad dake ziyara a Lebanon, tare da mai masaukinsa shugaba Emile Lahoud, sun yi misali da kudurorin MDD dake kiran Isra'ila ta janye daga yankunan Larabawa da ta mamaye a shekarar 1967 ta kuma janye daga kudancin Lebanon.

Sanarwar hadin guiwar ta ce cimma "zaman lafiya kammalalliya, mai adalci kuma mai dorewa" ta dogara kan aiwatar da kudurorin MDD.

Kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna kai idan shugaba Hosni Mubarak na Masar ya gana da shugaba Bush ranar talata a nan Washington. Shugaba Mubarak ya iso nan Washington ranar asabar tare da maidakinsa.

XS
SM
MD
LG