Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka A Zauren Taron Commonwealth Sun Hada Kai A Bayan Zimbabwe - 2002-03-03


Shugabannin Afirka suna yin turuwa wajen goyon bayan Zimbabwe, yayin da kasashen turawa membobin kungiyar Commonwealth suke son dakatar da kasar daga cikin wannan kungiya ta kasashe renon Ingila, kafin zaben da za a yi a can Zimbabwe.

Wannan batu ya shanye kan shugabannin gwamnatocin kasashen Commonwealth a rana ta biyu ta taron da suke yi a Coolum, a kasar Australiya.

Ministan yada labarai na Zimbabwe, Jonathan Moyo, ya zargi firayim minista Tony Blair na Britaniya da laifin jagorancin kyamfe na bambancin launin fata a kan kasar da tayi wa mulkin mallaka. Mr. Moyo ya fito da kakkausar harshe yana sukar zarge-zargen da Mr. Blair yake yi wa shugaba Robert Mugabe a zaman "babban abin kunya, kuma maras karbuwa."

Firayim ministan na Britaniya yayi kiran da a dakatar da Zimbabwe daga cikin kungiyar a saboda zargin shirya yin magudi kafin zaben shugaban kasar da za a yi a can.

A halin da ake ciki, Firayim minista Jean Chretian na Canada, ya shaidawa 'yan jarida a yau lahadi cewa kowa ya yarda ba za a dauki wani mataki a kan kasar Zimbabwe ba kafin zaben.

Shugaba Mugabe yana fuskantar kalubale daga madugun 'yan adawa Morgan Tsvangirai a zaben na ranakun 9 da 10 ga watan nan na Maris.

XS
SM
MD
LG