Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bayan Da Shugabannin Afirka Suka Ce ba Su Yarda Ba... - 2002-03-04


Shugabannin kasashen kungiyar "Commonwealth" sun jinkirta yanke shawara a kan ko zasu dakatar da kasar Zimbabwe daga cikin wannan kungiya mai wakilai 54, a saboda tashin hankalin siyasa a wannan kasa dake yankin kudancin Afirka.

Shugabannin na "Commonwealth" dake ganawa a garin shakatawa na Coolum a gabashin Australiya, sun yarda zasu kafa wani kwamiti mai wakilcin kasashe uku domin auna zaben da za a yi a Zimbabwe a ranakun 9 da 10 ga wannan wata, su kuma dauki mataki idan har ba a yi wannan zabe tsakani da Allah ba.

A cikin wata sanarwa, shugabannin sun bayyana damuwa sosai da tashe-tashen hankula da kuma cin zarafin siyasa dake wakana kafin zaben shugaban kasar, sun kuma yi kira ga dukkan sassan kasar da su kaucewa tashin hankali.

Wannan shawara ta biyo bayan adawa sosai da shugabannin Afirka a zauren taron suka nuna ga kiran da kasashen Britaniya, da Canada, da Australiya da kuma New Zealand suka yi cewar a dakatar da Zimbabwe nan take.

A jiya lahadi ministan yada labarai na Zimbabwe, Jonathan Moyo, ya ce kasashen dake neman da a dakatar da Zimbabwe suna yin haka ne domin bambancin launin fata kawai.

A can Zimbabwe dai, shugaba Robert Mugabe da babban mai adawa da shi Morgan Tsvangirai sun shiga mako na karshe na yakin neman zabe. Mr. Mugabe, mai shekaru 78 da haihuwa, shi yake mulkin kasar Zimbabwe tun lokacin da ta samu ’yanci daga Britaniya a shekarar 1980.

XS
SM
MD
LG