Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe Sojojin Amurka 9 A Afghanistan - 2002-03-04


Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an kashe sojojin Amurka su akalla tara a gabashin Afghanistan, a lokacin da 'yan ta'addar al-Qa'ida da abinda ya rage na dakarun Taleban suka bude wuta kan wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu na sojan Amurka.

A jiya lahadi da maraice, wani jirgin yaki mai saukar ungulu yayi saukar gaggawa, a bayan da aka harbo shi a kudu da garin Gardez, ya kuma kashe sojoji su akalla shida. Ba a san ko sojojin na Amurka sun mutu a lokacin da jirgin ya subuto kasa ba ne, ko kuma a lokacin fadan da aka gwabza da sojojin dake cikinsa daga baya.

A wani lamarin da ya faru a wannan yankin kuma, an kashe wani sojan Amurka a lokacin da wani jirgi mai saukar ungulu ya sauko babu shiri kafin ya sake tashi.

An raunata wasu sojojin Amurka da ba a san yawansu ba a wadannan al'amura biyu.

Wadannan jiragen yaki biyu masu saukar ungulurufawa sojojin da Amurka ke yiwa jagoranci baya ne a gwabzawar da suke yi gaba da gaba da dakarun al-Qa'ida da na Taleban a kudu da garin Gardez.

Jiragen saman yaki na Amurka suna yin luguden bam kan wuraren da abokan gabarsu suka ja daga, a wani bangare na farmakin da aka kaddamar ranar Jumma'a da maraice.

An tabbatar da kashe sojan Amurka daya da mayakan Afghanistan uku ranar asabar a lokacin da mayakan al-Qa'ida da Taleban suka turje, suka yi kememe a wuri guda.

Jami'an Amurka sun ce mayakan al-Qa'ida da na Taleban da suka rage sun sake taruwa wuri guda a cikin jerin kogunan duwatsu da ramukan karkashin kasa dake kusa da garin Gardez a lardin Paktia. Jami'an Afghanistan a yankin sun ce mayakan sun kai dubbai.

Wannan farmaki shine mafi girma da aka kaddamar a Afghanistan a cikin wannan shekara, kuma ya kunshi sojoji dubu 1 da 500 na Afghanistan, da Amurka da na kasashen kawance. Kasashen kawance da dama suna cikin wannan farmaki cikinsu har da Australiya, da Canada, da Denmark, da Faransa, da Jamus da kuma Norway.

XS
SM
MD
LG