Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zub Da Jini Ya Karu A Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza - 2002-03-04


Sojojin Bani Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 17 yau litinin a yankin Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza.

Wannan zub da jini ya samo asali ne daga hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu sansanonin ’yan gudun hijira biyu na Falasdinawa, hare-haren da aka ce martani ne kan wadanda suka kashe yahudawa 22 a shekaranjiya asabar da jiya lahadi.

A garin Ramallah na yankin Yammacin Kogin Jordan, jami’an Falasdinawa sun ce mutane 6 sun mutu, wata mace guda tare da yara kanana biyar, a lokacin da Isra’ila ta cilla rokoki kan wasu motoci biyu.

Mutane akalla bakwai sun mutu a lokacin da aka yi dauki-ba-dadi a sansanonin ’yan gudun hijira na Jenin da Rafah. Falasdinawa suka ce daga cikin wadanda aka kashe har da wani jagoran kungiyar nan da ake kira ‘Birged Din ’yan Shuhada’u na al-Aqsa’.

A wani lamarin da ya faru a kusa da Nablus a yankin Yammacin Kogin Jordan kuma, sojojin Isra’ila sun bindige suka kashe wani Bafalasdine wanda aka ce ya ruga ya doshi wani wurin da sojoji ke binciken mutane da ababen hawa.

XS
SM
MD
LG