Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Amurka Sun Ci Gaba Da Kai Raraka a Gabashin Afghanistan - 2002-03-05


Jiragen saman yakin Amurka sun sake kai hare-haren bam kan wuraren da 'yan al-Qa'ida da Taleban suka yi tunga a gabashin Afghanistan.

Wannan farmaki na baya-bayan nan ya zo a bayan da sojojin Amurka da na Afghanistan dake kawance da su, suka yi kokarin tumbuko wadannan mayaka a ranar litinin daga inda suka yi tunga a tsaunukan lardin Paktia mai iyaka da kasar Pakistan.

Jami'an tsaron Amurka sun ce an kashe sojojin Amurka 8, aka raunta wasu guda 40 tun lokacin da aka kaddamar da wannan farmaki mai suna "Operation Anaconda" a ranar Jumma'a.

Kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, Janar Tommy Franks, ya ce an kashe mayakan al-Qa'ida da na Taleban har 200, yayin da aka kama wasu ana yi musu tambayoyi.

XS
SM
MD
LG