Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Charles Taylor Da Mukarrabansa Suna Iya Fuskantar Sabon Takunkumi - 2002-03-05


Babban jami'in dake kula da al'amuran Afirka a gwamnatin shugaba Bush ya ce watakila nan bada jimawa ba Majalisar Dinkin Duniya, MDD, zata sanyawa shugaba Charles Taylor na Liberiya da manyan mukarrabansa sabbin takunkumi.

Mataimakin sakataren harkokin waje mai kula da harkokin nahiyar Afirka, Walter Kansteiner, ya shaidawa Muryar Amurka cewa zai yiwu nan bada jimawa ba MDD zata tattauna batun sanya takunkumi kan masana'antun katako na Liberiya, inda Mr. Taylor yake da hannu sosai.

Ya ce takunkumin da ake aiki da shi a yanzu, ya takaita ribar da Mr. Taylor yake samu daga yin cinikin duwatsun lu'ulu'u a bayan fage, da kuma tasirinsa na tallafawa 'yan tawayen Saliyo da Guinea.

Amma kuma, kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce ribar da Mr. Taylor yake samu daga cinikin katako tana ba shi sukunin ruruta wutar yaki a Afirka ta Yamma.

A shekarar da ta shige MDD ta kafa takunkumi, takaitacce, a kan Mr. Taylor da manyan mukarrabansa. Har ila yau majalisar ta nemi kamfanonin sarrafawa da cinikin duwatsun lu'ulu'u a fadin duniya da su taimaka wajen kawo karshen satar cinikin duwatsu na haramun.

XS
SM
MD
LG