Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Suna Ci Gaba Da Kai Farmaki A Yankunan Falasdinawa - 2002-03-06


Sojojin Isra'ila sun kara kai hare-hare kan cibiyoyin Falasdinawa a yankin Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza.

Jiragen saman yakin Bani Isra'ila sun kai hari kan ofishin kungiyar Fatah, ta shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, a kusa da birnin Hebron dake Yammacin Kogin Jordan. An harba wani makami mai linzami kan ginin ofishin yau laraba a garin Dahariya, wanda Falasdinawa ke gudanar da mulkinsa a kudu da birnin Hebron. Babu wani rahoton da aka samu na jin rauni.

Tun kafin wannan lokaci kuwa, jiragen yakin kai farmaki na Isra'ila sun raraki wani gini na jami'an tsaron Falasdinawa a birnin Gaza, yayin da sojoji a kasa suka yi ta kai farmaki a sassa dabam-dabam na Zirin Gaza.

Sojojin Isra'ila dake samun rakiyar tankokin yaki, sun kai farmaki a sassan arewaci, da tsakiya da kuma kudancin Zirin Gaza. Rundunar sojan Bani Isra'ila ta ce tana kokari ne ta ragargaza abinda ta kira “kungiyoyin ta'addanci na Falasdinawa” a Gaza.

Jami'an Falasdinawa sun ce an kashe mutane akalla bakwai a gwabzawa da sojojin Isra'ila.

Wannan matakin sojan Isra'ila ya biyo bayan kazamin fada da zub da jinin da aka yi ranar talata, ciki har da harba roka da Falasdinawa suka yi a kan wani gari na Isra'ila.

A wani lamarin dabam a yankin Yammacin kogin Jordan kuma, sojojin Isra'ila sun harbe suka raunata wasu Falasdinawa biyu wadanda a cewarsu, sun yi kokarin kutsawa ta cikin shingen bincike da sojoji suka kafa a Maccabim.

XS
SM
MD
LG