Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pentagon Ta Ce An Kashe Daruruwan Mayakan Taleban Da al-Qa'ida - 2002-03-06


Rundunar sojojin Amurka ta ce an kashe daruruwan sojojin Taleban da al-Qa'ida, a yayin da sojojin kawancen da Amurka take yi wa jagoranci suka ci gaba da kai farmaki a yau laraba a tsaunukan gabashin Afghanistan.

Wani kakakin soja, Kanar Walter Piatt, ya ce sojojin kawance sun kashe mayakan abokan gabarsu har 350. Ana kiyasin cewa mayakan Taleban da al-Qa'ida wadanda suka buya tare da iyalansu a tsaunukan Arma na gabashin Afghanistan sun kai 500 zuwa 700.

Jami'ai suka ce ci gaba da kai hare-hare ta sama yana nakkasa kwarin guiwar mayakan, amma har yanzu suna nuna turjewa sosai.

A halin da ake ciki, da asubahin yau laraba ne gawarwakin sojojin Amurka takwas da aka kashe a fada na baya-bayan nan suka iso nan Amurka.

XS
SM
MD
LG