Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Ya Soki Manufofin Ariel Sharon - 2002-03-06


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya soki yadda firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, yake yakar Falasdinawa, yana mai cewa ya kamata ya sake tunani game da wannan manufa ta sa.

A cikin furucin da yayi ga wani kwamitin majalisar dokoki a nan Washington, sakataren harkokin wajen ya ce tilas ne Mr. Sharon yayi tunani sosai kan wadannan manufofi nasa, ya ga ko zasu yi aiki. Sakatare Powell ya ce ayyana yaki kan Falasdinawa tare da karkashe duk wadanda za a iya kashewa, ba zai kai ko'ina ba.

Ya ce dukkan sassan su na bin manufofin dake kara tashin hankali. Ya ce shugaban Falasdinawa zai iya, kuma tilas ne ya kara daukar matakan kawo karshen hare-haren da Falasdinawa ke kaiwa kan 'yan Isra'ila.

Firayim minista Sharon ya fada a ranar litinin cewa tilas ne a ragargaji Falasdinawa sosai, a yi musu barnar rayuka da yawa kafin a iya komawa kan teburin shawarwari.

A can Majalisar Dinkin Duniya kuma, babban sakatare Kofi Annan ya ce wannan lamari na yankin Gabas ta Tsakiya yayi muni sosai. Ya ja kunnen shugabannin Isra'ila da falasdinawa cewa na baya ba zasu taba yafe musu ba idan har ba su kawo karshen wannan mummunan ukubar da suka jefa al'ummarsu ciki ba.

XS
SM
MD
LG