Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tura Karin Sojoji Zuwa Bakin Daga - 2002-03-06


Kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan ya ce ya kara dakaru metan zuwa 300 kan sojoji su kimanin 800 wadanda tun farko suka fara kai farmaki a gabashin Afghanistan. Har ila yau, Janar Tommy Franks, ya shaidawa 'yan jarida a nan Washington cewa an kai karin jirage masu saukar ungulu na farmaki zuwa bakin daga.

Tun da fari, wani kwamandan sojojin Amurka a bakin daga ya ce yawan abokan gabarsu ya ninku har sau uku tun daga ranar Jumma'a, a bayan da shugabannin kabilun yankin masu kishin addini suka yi kiran da a ayi jihadi kan Amurka.

Manjo janar Frank Hagenbeck ya ce rahoton leken asiri na Amurka ya nuna cewa mayakan al-Qa'ida da na Taleban su 600 zuwa 700 sun kutsa cikin yankin da aka ja daga, a kusa da bakin iyakar Afghanistan da Pakistan.

XS
SM
MD
LG