Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo Ya Nada Sabon Sufeto-Janar Na 'Yan Sanda - 2002-03-06


A bayan ganawar da yayi da dukkan gwamnoni 36 na Nijeriya a yau laraba, shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya cire sufeto-janar na 'yan sandan kasar, Musiliu Smith, ya maye gurbinsa da Tafa Balogun.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Abuja, Musa Muhammad, ya ce an kuma ba da sabon sufeto-janar Balogun karin iko na gudanar da gyare-gyare a cikin rundunar 'yan sandan Nijeriya.

Haka kuma, shugaba Obasanjo ya nada Kanu Agabi a zaman sabon ministan shari'a domin ya maye gurbin Bola Ige, wanda wasu 'yan bindiga suka kashe a cikin watan Disamba.

An kuma nada Olu Agunloye a matsayin mukaddashin ministan tsaro mai kula da rundunar mayakan ruwa, yayin da Dupe Adelaja zai karbi tsohuwar kujerar Mr. Agabi ta ma'aikatar albarkatun kasa.

Wadannan canje-canje suna zuwa ne a daidai lokacin da ake kara daukar matakan tsaro a ofisoshin jakadancin kasashen waje dake Nijeriya, bayan da wata kungiya ta umurci jami'an jakadanci su bar kasar nan da karshen makon nan, ko kuma su kuka da kansu.

Ministan yada labarai, Jerry Gana, ya shaidawa Muryar Amurka cewa an umurci hukumomin leken asiri da sauran na tsaro a Nijeriya da su farauto wadanda suka rubuta takardar barazanar ga ofisoshin jakadancin kasashen waje.

Wakilin Sashen Hausa a Abuja, Musa Muhammad, ya ce an kara daukar matakan tsaro a ofisoshin jakadancin kasashen waje dake Nijeriya domin kare abkuwar duk wani abu.

XS
SM
MD
LG