Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Rana Ta Karshe Ta Yakin Neman Zabe a Zimbabwe - 2002-03-08


Yau (Jumma'a) an shiga rana ta karshe ta zazzafan yakin neman zaben da ake yi a asar Zimbabwe, inda shugaba Robert Mugabe da mai kalubalantarsa, Morgan Tsvangirai, zasu gudanar da tarukan siyasa dabam-dabam.

Shugaba Mugabe zai yi jawabi ga wani taron magoya-bayansa a garin Bindura, mai tazarar kimanin kilomita 100 arewa da Harare, babban birnin kasar. Wannan yanki wata tunga ce ta magoya-bayan jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar. An ce ana kwasar magoya-bayan jam'iyyar ta motoci ana kaisu garin daga sauran garuruwan yankin domin su halarci wannan gagarumin taro.

A halin da ake ciki kuma, Mr. Tsvangirai zai gudanar da na sa yakin neman zaben a wata gunduma mai masana'antu dake birnin Harare, yankin da masu fashin bakin al'amurra suka ce yana da dinbim magoya baya. To amma kuma babu tabbas ko 'yan sanda zasu bari ya gudanar da wannan taro.

A jiya alhamis ma, sai da 'yan sandan suka tilastawa shugaban na 'yan adawa ya sauya wurin wani taro da zai yi da 'yan jarida, saboda sun ce taron haramtacce ne. Mr. Tsvangirai ya shedawa manema labaran cewa jam'iyyar shugaba Mugabe ta yi kokarin abin da ya baiyana a zama “yin duk wani siddabaru” domin ta tabbatar da samun nasara a wannan zabe.

Mr. Mugabe ya ce, watakila gwamnatinsa ta tuhumi Mr. Tsvangirai da aikata wasu laifuka bayan zaben, musamman ma zargin shirya makircin halaka shugaban. Mr. Tsvangirai ya musanta wannan zargi.

A gobe asabar da jibi lahadi ne za a gudanar da zaben. Mr. Tsvangirai ne dan takarar da ya fi yi wa mulkin Mr. Mugabe na shekaru 22 kalubale tun bayan da shugaban ya kama ragamar mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG