Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Sun Ce Kotu Ta Bada Umurnin Kara Wa'adin Jefa Kuri'a - 2002-03-10


Wani lauya na jam'iyyar adawa ta kasar Zimbabwe, ya ce kotun kolin kasar ta bada umurnin a kara tsawon lokacin jefa kuri'a zuwa rana ta uku, a zaben shugaban kasa mai dimbin tarihi a kasar.

Tun da fari, jam'iyyar adawar ta bukaci da a kara lokacin a bayan da ya bayyana a fili cewa akwai dubban mutanen da ba za su iya jefa kuri'unsu ba ya zuwa lokacin da za a rufe rumfunan zabe yau lahadi.

Ita ma tawagar 'yan kallon zabe daga Kungiyar Kasashe Renon Ingila, watau "Commonwealth," ta bada shawarar kara wa'adin jefa kuri'ar, tare da kara ma'aikata a rumfunan zabe domin gaggauta yadda ake kada kuri'u.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ambaci lauyan 'yan adawar yana fadin cewa gwamnati ta lashi takobin daukaka karar wannan hukumci. Amma babu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskata wannan rahoto.

A ranar asabar, dubban masu jefa kuri'a a birane da manyan garuruwa sun shafe sa'o'i da da yawa, wasu har sa'o'i 30, suna tsaye kawai a layi suna jiran jefa kuri'unsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Harare, babban birnin kasar, sun ce wannan jinkiri da ake samu a rumfunan zabe, wani bangare ne na makarkashiyar da aka kulla domin tabbatar da cewa shugaba Robert Mugabe yayi nasara a zaben.

Gwamnati ta rage yawan rumfunan zabe a alkaryu, inda 'yan adawa suke da karfi, suka kara yawan wadanda ke karkara, inda shugaba Robert Mugabe ya fi kwarjini.

A halin da ake ciki, kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Zimbabwe Human Rights Forum" mai zaman kanta, tana fadin cewa an kama mutane akalla 58 aka tsare su lahadin nan, a wasu matakai na tursasawa 'yan adawa.

Jami'an gwamnati sun sha musanta zargin musugunawa 'yan adawa tare da kokarin yin magudi.

A duk tsawon shekaru 22 da yayi kan karagar mulki, shugaba Robert Mugabe bai taba fuskantar barazana ga mulkinsa kamar irin wannan da yake fuskanta daga Morgan Tsvangirai ba.

XS
SM
MD
LG