Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartaswar Isra'ila Ta Goyi Bayan Kara Zafafa Farmaki - 2002-03-10


Majalisar zartaswar Isra'ila ta yanke shawarar kara zafafa farmakin sojan da kasar ke kaiwa a kan Falasdinawa, a bayan da Bani yahudu 14 suka mutu, wasu fiye da 100 suka ji rauni, a wani sabon harin kunar-bakin-wake da harbe-harbe a ranar asabar.

Yau lahadi da safe, makamai masu linzami na Isra'ila sun lalata hedkwatar shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a Gaza. Makamai masu linzami akalla 30 suka abka kan wannan gini, wanda a cikin shekarun baya Malam Arafat yayi amfani da shi wajen karbar bakuncin shugabannin kasashe da wasu jami'an. Ba ya wurin a lokacin da aka kai harin. Sojojin Isra'ila sun shafe watanni ukun da suka shige suna hana Malam Arafat barin ofishinsa dake Ramallah.

Duk da lalata ginin da aka yi sosai, babu wanda ya ji rauni mai muni a wannan hari a zirin Gaza.

Firayim minista Ariel Sharon ya sake fadin cewa Isra'ila tana bakin yaki ne, kuma tilas ta ci gaba da nuna hadin kai a saboda abinda ya kira ta'addancin da ake yi mata. A daidai wannan lokacin kuma, ya ce har yanzu Isra'ila tana da burin ganin an cimma tsagaita bude wuta.

An ci gaba da samun tashe-tashen hankula jefi-jefi a yau lahadi. Jiragen saman yaki na Isra'ila sun sake kai hari, inda suka ragargaza wani ginin hukumomin tsaron Falasdinawa a kusa da birnin Gaza. Har ila yau a Gaza, wani Bafalasdine ya bude wuta kan Bani yahudu a kusa da kofar shiga cikin wata unguwar Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna, inda ya raunata mutane maza biyu, dayansu rauni mai muni, kafin shi kuma a bindige shi har lahira.

Kungiyar 'Yan Shuhada'u na al-Aqsa, mai alaka da kungiyar Fatah ta malam Arafat, ta dauki alhakin kai wannan harin.

Wannan tashin hankali na baya-bayan nan ya biyo karshen mako mfi muni a yankin, tun daga lokacin da fada ya barke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa watanni 17 da suka shige. Akalla, an kashe Falasdinawa 100 da 'Yan Isra'ila 50 a cikin makon da ya shige.

XS
SM
MD
LG